Matsalar Tsaro : ƴan bindiga suka sace yara ƴan makaranta a Katsina
Wasu ƴan bindiga haye kan babur sun yi garkuwa da wasu yara maza ɗalibai guda biyu da ke kan hanyarsu ta zuwa ƙaramar makarantar sakandire da ke garin Babban Duhu a ƙaramar hukumar Safana da ke jihar Katsina.
Wani malamin makarantar wanda ba ya son a ambaci sunansa ya shaida wa BBC cewa al’amarin ya faru ne da safiyar ranar Alhamis ɗin nan, inda ƴanbindigar suka yi awon gaba da yaran guda huɗu kafin daga bisani yara biyu su tsere.
“Yaran sun taho daga wani gari da ake kira Barebari inda ƴanbindigar haye a kan mashina guda huɗu suka yi garkuwa da yara huɗu ne kafin biyu daga ciki su tsere.
Sun yi garkuwar ne a wani wuri mai nisan kilomita kimanin biyu daga makarantar wa.”
A wane hali yaran suke ciki?
Har zuwa yammacin ranar Alhamis lokacin da BBC ta tattauna da malamin babu cikakkiyar masaniyar inda yaran da aka sace suke “har kawo yanzu ba bu labarin cewa ƴanbindigar sun kira iyalan yaran domin neman kuɗin fansa.”
Babu kuma wani bayani da ke nuna cewa jami’an tsaro sun bi ƴanbindigar domin ceto yaran guda biyu da suka yi garkuwa da su. Domin mu dai mun sanar da su ta hanyar lambar kira da aka ba mu idan irin wannan ta faru mu sanar da su”, kamar yadda malamin ya yi ƙarin bayani.
Sai dai jami’an tsaro da gwamnati sun sha fadin cewa suna ɗaukar matakai da ba lallai jama’a su sani ba kuma suna ba su nasara a kan ƴanbindigar.
Halin da makarantar ke ciki
Malamin ya shaida wa BBC cewa “yanzu dai mun samar da sakataren Ilimi na ƙaramar hukumar Safana cewa za mu kulle makarantar har zuwa ranar Litinin domin mu samu nutsuwa sannan iyayen yara ma su samu nutsuwa.”
Dangane da kuma da halin da iyayen yara ke ciki sakamakon garkuwa da ƴan makarantar malamain ya ce “e gaskiya dole ne akwai fargaba a al’amarin duk da ma dai iyayen na ƙaƙarin aiko yaransu makarantar. Amma dai dole ne abin ya tsorata su.
Ina ganin makomar ilimi a wannan makarantar ita ce idan har gwamnati ta iya ceto yaran nan guda biyu da aka sace, to iyayen yara za su samu ƙwarin gwiwar barin yaransu su ci gaba da zuwa makaranta. Sannan kuma ya kamata gwamnati ta samar da tsarin da zai tabbatar da tsaron waɗannan makarantu.” In ji malamain makarantar.
BBC Hausa