Mai amfani da shi ƙanin Malam Gadon Kaya ya shiga hannu, yana damfarar al’umma
Wannam bawan Allah da kuke gani dan damfara ne, ya dauki tsawon lokaci yana amfani da sunan Adnan a matsayin wai shi kanin Sheikh Dr Abdulllah Usman Gadon kaya ne, yana damfaran mutane kudi da kayan abinci
Yana bin manyan mutane ya karbi bashin kudi da sunan Sheikh Abdallah, yana zuwa gurin manyan ‘yan kasuwa a Kano, Katsina da Kaduna ya karbi kaya da sunan Sheikh Abdallah
Sheikh Abdallah yace daga ko’ina ana kiransa ace masa kaninsa Adnan yazo ya karbi bashin kudi ko kaya da sunansa, wannan mutumin ba karamin cutar da Malam yayi ba
Malam ya sha fitowa a gurin karatu yana magana akan wannan azzalumi dan damfara, ya cuci mutane masu yawa da sunan Malam
Asirinsa ya tonu, ‘yan sanda sun kamashi, yana ofishin ‘yan sanda dake Gwale Division, ana kira ga al’ummah duk wanda ya san wannan mutumin ya damfareshi da sunan Malam to ya je Gwale Division
Ku dubi mutumin nan girma ya fara kamashi, yana da mata da iyalai amma yake ciyar dasu da dukiyar haran, kunga karshensa bata yi kyau ba, ya bata tarihin rayuwarsa da na iyalansa saboda mutuwar zuciya, to wannan ya kamata ya zama darasi garemu
A rayuwa ba zau yiwu ka wanzu kana cutar da al’ummah kuma kayi tunanin asirinka ba zai tonu ba, ko ba don mutuncin kanka ba ka tuna ‘ya’yanka da matanka, kar kayi abinda zasuyi nadamar saninka, uwa uba tsoron Allah Ya na gaba da komai
Muna rokon Allah Ya tsare mana imanin mu
Ga zantawarsa da hukumar yan sanda.