Atiku Ya Caccaki Tinubu : Uƙubar T-Pain ko yara basu tsira ba
Jagoran Talakawan Nigeria Maigirma Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar ya caccaki Gwamnatin Tinubu kan alhakkin yaran Arewa kanana da ta dauka saboda sun yi mata zanga-zangar neman sauyi daga kuncin rayuwa
Atiku yace hankalinsa ya tashi matuka bayan yaga an kawo yara kanana Kotu cikin wani yanayi mai ban tausayi sakamakon yunwa da ta yagalgalasu bayan an kamasu saboda sun yi zanga-zanga
Atiku yace yanayin da ya ga yaran ya tuna masa da bakin tarihin sansanin ‘yan gudun hijira na Sojojin Nazi a Kasar Jamani inda yunwa ta dinga kashe yara kanana a shekarun 1937
Atiku yace an tsare yara sama da wata uku saboda sun fito neman ‘yanci akan mayuwacin hali da aka jefa su, maimakon a saurari kukansu sai aka saka musu da mugunta da ukuba
Atiku yace kowace Kasa za’a mata bahasi ne game da yadda take kula da jama’ar Kasar musamman masu karamin karfi, amma abin bakin ciki ne ace yanzu a wannan Kasar hatta yara kanana da basu balaga ba basu kubuta daga cutarwan T-PAIN ba, inji Atiku
Hakika Atiku ya cika jagora, muryansa ne kadai yanzu ta rage wa talakawan Nigeria, shiyasa ban taba da na sanin kasancewa a gidan siyasar Atiku ba
Ubangiji Allah Ka rabamu da T-PAIN lafiya