Ƴan Nijeriya miliyan 33 za su kamu da yunwa a sabuwar shekara – Rahoto
Rahoton Cadre Harmonisé na watan Oktoba ya yi hasashen cewa akalla mutane miliyan 33.1 a jihohi 26 da Babban Birnin Tarayya Abuja za su fuskanci matsalar karancin abinci tsakanin watan Yuni zuwa Agusta na shekarar 2025.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya rawaito cewa wannan hasashen ya fito ne daga Rahoton Nazarin CH da aka fitar ranar Juma’a a birnin Abuja.
Nazarin an gudanar da shi ne ta hanyar hadin gwiwa tsakanin Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Dinkin Duniya , Shirin Abinci na Duniya (WFP), Ma’aikatar Noma da samar da Abinci ta Tarayya, da sauran abokan hulɗa.
Jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Sokoto, Zamfara, Borno, Adamawa, Yobe, Gombe, Taraba, Katsina, Jigawa, Kano, Bauchi, Plateau, Kaduna, Kebbi, Neja, da kuma Benuwai.
Sauran jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Cross River, Enugu, Edo, Abia, Kogi, Nasarawa, Kwara, Ogun, Legas, Ribas, da Babban Birnin Tarayya (FCT).
Rahoton ya nuna cewa wannan adadin ya haɗa da mutane 514,474 da aka raba da matsuguninsu a Borno, Sokoto, da Zamfara.
Ya bayyana cewa kimanin mutane miliyan 25 a cikin jihohi 26 da FCT suna fuskantar matsalar abinci a yanzu haka.