Labarai

Yanzu -Yanzu : farashin man fetur yayi tashi gwauron zabi ya kai ₦1,030 ko wace lita a gidan man NNPC a Abuja



FCT, Abuja – Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi a gidajen mai mallakin kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) da ke Abuja.

Farashin ya tashi zuwa Naira 1,030 kan kowace lita a gidajen mai na kamfanin NNPCL da ke Abuja a ranar Laraba

Wannan ci gaban na baya-bayan nan ya zo ne bayan da kamfanin NNPCL ya yanke shawarar kawo ƙarshen yarjejeniyarsa da matatar man Dangote.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa gidajen man NNPCL da ke tsakiyar babban birnin tarayya Abuja, sun daidaita farashin man fetur zuwa N1,030.

Wata kwastoma da ta je siyan man mai suna Glory Okoye, ta tabbatar da cewa tuni aka canza farashin zuwa N1,030 kan kowace lita.

“Wannan abin dariya ne. Na lura cewa farashin kowace lita ya canza daga N897 zuwa N1,030.”
– Glory Okoye

A wasu gidajen man da dama na NNPCL da ke unguwannin Wuse da Lugbe a birnin Abuja, farashin kowace lita ɗaya ya koma N1,030.

Asali: Legit.ng









Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button