Labarai

Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zanga a Abuja (bidiyo)

Jami’an ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja sun harba barkonon tsohuwa a zanga-zangar “Fearless In October” kan rashin shugabanci na gari a Abuja a yau 1 ga watan Oktoba.

Masu zanga-zangar sun taru ne a unguwar Utako da ke Abuja, suna daga tutar Najeriya Green-Fara-Green da kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban kamar

“EndBadGovernance”, “DiasporaVoting”, “EndHighLivingCosts”, da dai sauransu amma ‘yan sanda suka tarwatsa su.LIB sun ruwaito.

Hotunan bidiyo da aka yada ta yanar gizo sun nuna masu zanga-zangar suna gudu da skelter bayan an harba barkonon tsohuwa don tarwatsa su.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button