Labarai

Yadda Shekarau ya ƙwace fulotin da ya bayar a gina makarantar Islamiyya a Kano

Advertisment

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ƙwace wani fuloti da ya bayar sadaka domin gina makarantar Islamiyya a unguwar Sabuwar Gandu da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa Shekarau ya sadaukar da fulotin ga makarantar Islamiyya mai suna Imam Malik bin Anas li Tahfizil Quran wat Tarbiyya wa Ta’alim domin ci gaban ilimin addinin Musulunci.

Jaridar ta ce ta na kyautata zaton hukumar makarantar ce ta roki Shekarau da ya bada filin domin gina makaranta da Masallaci saboda ɗaliban ta a waje su ke karatu.Yadda Shekarau ya ƙwace fulotin da ya bayar a gina makarantar Islamiyya a Kano

A wata takardar shaidar sadaukar da filin, wacce Shekarau da kan sa ya sanya wa hannu a ranar 14 ga watan Agusta na 2021, tsohon Sanatan ya ce ya sadaukar da fulotin, wanda ke lamba 44, Layin Mai Unguwa, Sabuwar Gandu, Kumbotso.

A takardar, Shekarau ya ce ya bada umarnin cire filin daga dukiyarsa ta magada, inda ya jaddada cewa an bada filin ne don gina makaranta ba wani abun ba daban.

Sai dai wasu majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa Shekarau ne ya kwace filin ya sayar da shi, inda su ka shaida wa jaridar cewa tuni ma wadanda su ka siya su ka fara aiki a filin har sun rusa Masallacin da makarantar ta fara ganawa.

Sun kuma ce ba su taba tunanin cewa Shekarau zai Ya kyauta yankuna kwace abinda ya kyautar.

Sai dai kuma da aka tambayi Kakakin Shekarau, Sule Ya’u Sule ya ce mai gidan sa ba sayar da filin ya yi ba, inda aya kara da cewa, ya sa an sa shi a kasuwa sakamakon cin amana da shugabannin makarantar su ka yi.

A cewar Sule, malaman makarantar ne su ka fara yanka shaguna a maimakon gina makarantar Islamiyya kamar yadda su ka yi alkawarin da Shekarau.

Ya kara da cewa “hakan ne ya ɓata wa Maigida rai har ya ce a saka filin a kasuwa domin cin amana ne tantsa.

“Yanzu haka Sheikh Abdulwahab, wanda dama mutanen daliban sa ne, ya shiga maganar kuma ya tsne musu.

“Maganar da har ta sa an samu rarrabuwar kai kuma an ke kotu ma,” in ji Sule.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button