Mutane 120 sun maka mawaki P Diddy a Kotu kan zargin fyade da lalata da su


Mutane 120 za su maka wawakin gambara na kasar Amurka, Sean Combs, wannan aka fi sani da P Diddy a gaban kotu bisa zargin cin zarfi da lalata da su.
Mutanen da su ka hada da mata da maza, akwai kananan yara 25 a cikin su, sun zargi Combs da cin zarfinsu ta hanyar fyade da lalata da su.
An yi zargin yayi cin zarafin ne daga mafi yawa a lokutan bukukuwa daga 1991 zuwa wannan shekarar.
Tony Buzbee, wanda ke wakiltar masu kara, ya ce “Babban abinda yake a sirrance a masana’antar nishadi a yanzu ya zama ba sirri ba saboda a bayyana shi a duniya”.
Ya yi ikirarin cewa ana yawan cin zarafin kananan yara da sunan yi musu alkawarin samun nasara a fannin waka. Yaro daya ma da aka ci zarafi shekarun sa basu wuce 9. ” Wannan yaron, ana zargin Combs da cin zarafinsa ta hanyar lalata da shi a wajen buga wakoki, inda aka yaudare shi da alkawari shi da iyayen sa”, inji Buzbee.
Acewar, Buzbee, sama da mutane dubu 3 ne suka tuntubi kamfanin sa na shari’a kuma sun ce duk sun fada cikin mutanen da Combs yaci zarafin su. Bayan tattara zarge zargen ne, suka yanke shawarar wakilta 120 daga cikin su. Wasu batutuwan ma har yanzu ana sake duba a kansu.
Mawakin, na jiran a fara yi masa shari’a kan zargin lalata da fyade. Sai dai ya musanta zarge zargen. Lauyan dake kare shi ya ce mawakin zai wanke kansa.