Labarai

Matashi ya jefa ƴar shekara 16 a rijiya bayan ya mata fy@ɗe a Katsina

Advertisment

An kama wani matashi mai shekaru 24, mai suna Usman Mohammed Iyal bisa zargin yi wa ƴar shekara 16 fyade da yunkurin halaka ta ta hanyar jefa ta a cikin rijiya a cikin birnin Katsina.

LEADERSHIP ta rawaito cewa an dakile yunkurin wanda ake zargin ne a yayin da ‘yan sanda suka dau matakin gaggawa na bincike wanda ya kai ga ceto yarinyar daga rijiya.

Lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Satumba a yayin da mahaifiyarta ta aike ta.

Acewar rundunar yansandan jihar Katsina, wanda ake zargin da ke dauke da wuka ya yi wa yarinyar barazana tare da kai ta wani kango inda ya yi mata fyade.

A wani yunkuri na boye laifinsa, wanda ake zargin ya jefa yarinyar cikin rijiya bisa niyyar kashe ta.

Mahaifin yarinyar, Abdullahi Sabitu, ne ya kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yansanda.

‘Yansanda sun yi nasarar ceto yarinyar daga rijiyar tare da kama wanda ake zargin.

Yarinyar dai na ci gaba da karbar kulawar likitoci a yayin da ake ci gaba da bincike.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button