Kano : Yan sanda sun cafke matasa da zargin kashe uban gidansu da ƙone gawarsa saboda fili


Duniya ina zaki damu a kullum al’amarin kasar nan sai Baka mamaki yake ka duba wannan matasa mai gidansu wanda yake rage musu zafinta amma sunka kashe saboda kawai su mallaki filinsa innalillahi Wa’innah Alaihi Raj’un.
Rundunar ‘Yan sandan Jahar Kano ta kama wasu Matasa uku da suka hada da Aliyu Adamu da Mubarak Abdussalam da Kuma Sadik Sunusi da ake zarginsu da kisan wani Matashi Dahiru Musa me shekaru 32 a Unguwar Gaida ‘Yan kusa, bayan sun gayyace shi har gida suka bashi Shinkafar Bera a cikin Abinci, tare da caccaka masa wuka har ya mutu daga karshe suka bankawa gawarsa wuta.
Kakakin Rundunar Yan Sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawaya ne wallafa Labarin inda yake musu tambayoyi sunka amsa.
Ga bidiyon nan ku saurara kuji yadda al’amarin ya faru.