Labarai

Kano: Kotu ta daure wasu mutane 2 bisa laifin damfarar Dantata da ATM Gwarzo

Advertisment

Kotun majistare mai zamanta a Gyadi-Gyadi, Kano ta yanke wa Bukar Galadima da Suleiman Ahmed hukuncin daurin gidan yari bayan samun su da laifin zamba kan attajirin nan na Kano, Alhaji Aminu Dantata da kuma tsohon karamin ministan gidaje da ci gaban birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo.

Masu laifin sun yi hadin baki domin damfarar Dantata Naira miliyan 5, da Gwarzo Naira miliyan 1.

Galadima ya yi ikirarin cewa shi ne tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya, Injiniya Abba Gama, inda ya nemi taimakon kudi na magani daga wurin Dantata, wanda ya aika masa da naira miliyan biyar, sai daga baya aka gano cewa Gama bai nemi wannan bukata ba.

Dantata ya kai rahoton ga Hukumar Koke da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, inda aka kama Galadima da Ahmed aka gurfanar da su a gaban Mai Shari’a Umma Sani Kurawa, wadda ta same su da laifin hada baki wajen aikata zamba.

Kurawa ta yanke musu hukuncin daurin watanni shida ko biyan tarar naira dubu 30 da kuma watanni uku saboda kage ko tarar naira dubu 20, sai kuma wata shida ko tarar naira dubu 20 saboda cin amana.

Daily Nigerian Hausa

Advertisment

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button