Labarai
Ban taba aure ba, kuma nayi hotunan ne domin nishadi da yanci – Bala Muhammad (bidiyo)
Bala Muhammad wanda a baya bayan ya fara tashe a kafafen sada zumunta na zamani sakamakon faifayin hotunan badala da ya yi ta yadawa a shafinsa na Facebook da wasu mata a wani yanayi mai cike da zargi.
To saidai bayan ya shiga hannun hukumar HISBA a jihar Bauchi, Bala Muhammad ya nemi gafara.
“Hotuna ne wadanda anokaina na Facebook suka tono, wanda da na yi su tun shekaru goma da suka wuce, wadansu ma kusan shekaru ashiri, da ni da mata da nake nema saboda nishadi da dan nuna farin ciki na rayuwar nishadi da nake ciki.”Inji Bala Muhammad.
Ga bidiyo nan ku saurara.