Ba zai yiyu A Rika sayar da Litar man fetur ƙasa Dan ₦1350 Ba a Nijeriya – Rahoto
Bayan samun tataccen man fetur da ya kai lita miliyan 103 daga matatar mai ta Ɗangote a tsakankanin 15 da 30 ga watan Satumba, Kamfanin Mai na ƙasa, NNPC ya shirya tsaf domin sake fasalin farashin man kamar yadda wasu da ke da masaniya kan wannan yunƙuri suka shaida wa PREMIUM TIMES.
Matatar ta yi nasara bai wa motocin dakon mai 2,207 cikin 3,621 da suka je domin ɗaukar man. Motocin sun yi nasarar ɗibar lita 102,973,025 cikin lita 400,000,000 da aka tsara fitarwa daga cikin lita miliyan 25 a kullum da kamfanin ya yi alƙawarin tacewa. Wanda hakan ke nuna kaso 26% na irin ƙoƙarin da kamfanin ya yi kamar yadda PREMIUM TIMES ta gane wa idanunta.
Kamfanin NNPC ya fara dakon man ne daga matatar man Ɗangote a ranar 15 ga Satumbar 2024 a matsayin kamfanin da kaɗai zai riƙa cinikayyar mai da kamfanin kai tsaye.
A wannan rana dai, kamfanin ya fitar da sanarwa sayen mai daga daga wajen Ɗangote a kan Naira 898.78 na kowacce lita tare da sayarwa ga ‘yan kasuwa kan Naira 765.99 wanda hakan ke nuna ta sa tallafi na Naira 133 a kowacce lita da ta sayar musu.
Sai dai tun wannan lokaci ne ake cigaba da samun ƙaruwar farashin man a gidajen man NNPC ɗin a faɗin ƙasar nan, inda farashin ya kai Naira 855 zuwa Naira 897 a wasu wuraren.
Sai dai wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa a yanzu irin wancan man da kamfanin NNPC ya shigo da shi daga ƙetare ya ɗau ƙarewa, inda za ta fara dogara da man da za ta fara samu daga matatar Ɗangote, akwai yuwuwar kamfanin ya sake daidaita farashin da abin da ya siya daga matatar.
A halin yanzu dai ba a san yaya farashin zai kasance ba, kuma duk wani ƙoƙarin na samun babban jami’in yaɗa labarai an kamfanin NNPC, Femi Soneye, ta waya ya cutura domin bai ɗaga kiran da aka iya masa domin yin ƙarin haske kan wannan batu
Kodayake, kamfanin ya saki wani jadawali na farashi a ranar 16 ga watan Satumba, inda ya bayyana farashin yadda man zai kasance a gidajen mai a faɗin ƙasar nan bayan samun wancan mai na farko daga matatar man Dangote. Farashin, a jihar Legas, ya kama Naira 950.22 duk lita ɗaya, inda a jihar Ribas zai kama Naira 980.22 da Naira 992.22 a Abuja.
Sannan kamfanin ya nuna cewa za a sayar da shi wancan mai a kan Naira 999.22 a Arewa maso yamma, inda a Barno da sauran jihohin da ke Arewa maso Gabas za a sayar da man a kan Naira 1,019.
Har’ila yau, za a sayar da man a kan Naira 980.22 a jihohin Kudu-maso-gabas, sai kuma Naira 960.22 a kan kowacce lita a jihohin Kudu -maso-yamma (Oyo, Ogun, Ekiti, Osun, Ondo) .
Sai dai wani ɗan cikin gida a kamfanin NNPC, ya ce wannan farashi na 16 ga watan Satumba ya tashi daga aiki domin kuwa farashin kuɗin musayar kuɗi na cigaba da sauyawa, kuma ga batun tashin farashin man saboda yaƙin da ake yi a Gabas ta tsakiya.
Majiyar ta ce a yanzu farashin ya kai Dala 78 na kowacce gangar mai a yayin da ake canzar da Dalar a kan Naira 1660, don haka ba yadda za a yi farshin mai ya haura 135 a Najeriya.