Labarai
Ahmad Musa da Shehu Abdullahi sun dawo taka leda a Kano Pillars


Advertisment
‘Yan wasan Nijeriya Ahmed Musa da Shehu Abdullahi sun sake komawa taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars a kwantiragi mai gajeran zango a gasar Firemiya ta Nijeriya ta 2024/25.
An hangi hoton ‘yan wasan biyu a filin daukar horo a ranar Alhamis a yayin da kungiyar ke shirin karbar bakuncin Sunshine Starts a wasannin mako na 5.
Kungiyar ta Kano Pillars ta wallafa a shafin ta na X a yau Juma’a cewa Ahmed Musa da Shehu Abdullahi da Nazir Laja da sauran ‘yan tawagar sun dauki horo a shirin karawa a wasan mako na 5.
Ahmed Musa dai na sake shiga kungiyar ne a karo na 3 bayan ya taka leda a tsakanin 2009/10 da 2021.