Labarai

Tinubu ya fi karfin ya saci dukiyar Nijeriya — Minista

Karamin Minsitan Cigaban Matasa, Ayodele Olawande ya ce Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, mutum ne mai “da ya gaji arziki” saboda haka ba shi da sha’awar wawure dukiyar kasa.

VON ta rawaito cewa Olawande ya bayyana haka ne a taro na hadin gwiwa na ma’aikatar raya matasa ta tarayya a Abuja.

Ministan ya bukaci ƴan Najeriya da su yi hakuri da gwamnatin Tinubu, yana mai cewa nan ba da wani lokaci mai nisa ba za a samu sauye-sauye masu kyau.

“Ina rokon ku da ku yi hakuri da wannan gwamnati. Nan ba da dadewa ba kasar za ta samu kyakykyawan tsari kuma rayuwar ‘yan kasar za ta sauya.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba talaka ba ne, mutum ne da kowa ya sani cewa ya gaji arziki, don haka ba za a ce masa yana son wawure dukiyar Najeriya ba.

” Yana cikin dukiya kuma a sakamakon haka, ba ya sha’awar wawure dukiyar kasa,” in ji Ministan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button