Shahararren mawakin siyasar nan, Garba Gashuwa ya rasu a Kano
Allah Ya yi wa shahararren mawakin siyasar nan, Alhaji Garba Gashuwa rasuwa.
Ƴar marigayin ta shaida wa wakilin DAILY NIGERIAN HAUSA cewa mahaifin na su ya rasu yau da asuba a Asibitin Kwararru na Murtala da ke Kano.
Ta ce ya rasu bayan ya sha fama da jiyya.
A cewar ta, marigayi Gashuwa ya haura shekara 70 kafin rasuwar ta sa.
Ya rasu ya bar ƴaƴa 11, mata biyu da kums jikoki da dama.
Gashuwa ya shahara wajen yi wa masu mulki wakoki tun lokacin mulkin soja har zuwa na farar hula.
Mafi shahara a wakokin sa ita ce wacce ya yi wa shugaban ƙasa na soja a wancan lokacin, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Sannan ya yi wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari waka da kuma jam’iyyar sa ta ANPP lokacin yana yakin neman zabe a 2023.
Daily Nigerian Hausa na addu’ar Allah Ya gafarta masa, Ya kuma kyautata bayan sa.