Labarai
Nijeriya ce ta biyu a ƙarancin abinci a duniya — Bill Gates
Shugaban gidauniyar haɗaka ta Bill & Melinda Gates, Bill Gates, ya ce Najeriya ce kasa ta biyu a jerin kasashe masu fama da karancin abinci a duniya.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke zantawa da wata kwararriya a fannin yada labarai, Lara Adekoro, kan yanayin abinci mai gina jiki a Najeriya da kuma nahiyar Afirka.
Ya ce lamarin ya kara tabarbare wa je sakamakon sauyin yanayi da dai sauran matsaloli.
A cewarsa, filayen noma sun shafe sakamakon sauyin yanayi wanda ya haifar da tashin gwauron farashin abinci.
Ya ce gidauniyarsa tana aiki tare da Cibiyar Kiwon Lafiya da sauran masu ruwa da tsaki don kara fahimtar matsalar yunwa da yanayi ke haifarwa.
Daily Nigerian Hausa