Mutuwar zuciya : Yan sanda sun cafke matashi mai zuwa makabarta yana tone ƙabari yayi sata (hotuna)
Majiyarmu ta samu wani labari marar jin daɗi daga marubuci a facebook Datti assalafy ya wallafa wannan labari inda yake cewa.
Sunansa Dauda Sa’idu matashi ne dan shekara 21, da tsakar dare yake tafiya makabartan Kiristoci dake anguwar Yelwan Kagadama a cikin garin Bauchi ya tone kabari ya saci karfen rodi kamar yadda zaku gani
Da yake amsa laifinsa a State CID Bauchi, Dauda Sa’idu ya bayyana cewa yana zuwa ya sayar da rodin wa ‘yan gwangwan wanda yake amfani da kudin wajen sayan tabar wiwi da abinci
Matashin yaro kamar wannan imba mutuwar zuciya ba me zai kaishi cikin Makabarta ya tone ya cire rodi ko tsoro babu, wannan idan ya rika zai zama gawurtaccen dan fashi da makami marar tsoro
Yanzu dai Maigirma Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Bauchi ya bada umarni a gurfanar dashi a Kotu da zaran an kammala bincike
Allah Ka karemu daga mutuwar zuciya.
Ga hotuna nan.