Labarai

Mafi ƙarancin albashi: Kwanan nan ma’aikata za su fara warwasa wa — Gwamnatin Taraiya

Advertisment

Gwamnatin Tarayya ta ce nan ba da jimawa ba ma’aikata za su fara karɓar sabon mafi karancin albashi wanda ya ƙunshi ƙari mai tsoka.

Nkeiruka Onyejeocha, Karamar Ministan Kwadago da Samar da Aiki ce ta bayyana haka a wajen wani taro da ta shirya tare da kungiyar kwadago da ma’aikata a yau Juma’a a Abuja.

Taron na da nufin ƙara wa ma’aikata sanin Ajandar sabuwar Nijeriya ta wannan gwamnati tare da samun shawarwari daga ma’aikata da ƴan kwadago, jaridar Daily Nigerian Hausa

A cewar Onyejeocha, gwamnatin tarayya na ganawa da kwamitin bangarori uku a yau, da kuma shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya.

“Kungiyoyi ukun sun hada da kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), ƙungiyar yan kasuwa ta kasa (TUC), da kuma kungiyoyi masu zaman kansu, sun yi taro ne domin tattaunawa kan hanyoyin biyan sabon mafi ƙarancin albashi mai tsoka.

“Za a kammala wannan taro gobe, domin muna so mu kawo karshen batutuwan, domin su fara biyan kudi nan take,” in ji ta.

Daily Nigerian Hausa

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button