Kyan fuska ko nuna tsiraici ba abu ne mai tasiri a masana’antar shirya fina-finai ba – Ebun Hodo
Jaruma a masana’antar Nollywood, Ebun Hodo ta bayyana muhimmancin da baiwa da gogewa suke da ita fiye da siffa ta jiki a masana’antar shirya fina finai.
Jaridar THE NATION ta rawaito cewa a wata tattaunawa da Potpourru, Hodo tayi bayanin cewa kyawun fuska ko nuna tsiraici basu ne kadai hanyar samun nasara a masana’antar shirya fina finai ba.
Game da yadda za a yi nasara a masana’antar , ta ce “Akwai karin magana da ake fada na cewa ‘Kowa za a iya kiran sa amma kadan ake zaba’, shin kina cikin wacce aka zaba?
” Shin kina da sani kan abinda kike yi? Zaki iya yin abin da ya ce a shirin film”,inji ta.
Hodo ta kuma musanta cewa kyawun fuska na iya sawa a samu nasara, inda ta ce dogaro kan bayyanar tsiraici ba zai zama abu mai jimawa ba.
Daily Nigerian Hausa