Labarai
Kuɗin Man Fetur Ya Ƙaru Zuwa N1,200 a kano
Masu ababen hawa sun kafa dogayen layi a gidajen NNPCL da ke Kano domin shan mai
Farashin litar man fetur ya yi tashin gwauron zabo zuwa Naira 1,200 a gidajen mai a a Jihar Kano.
Stunned by thousands of storks flying over the sky in Gia Viễn dike, Ninh Bình – Nếm TV
Gidajen mai masu zaman kansu sun kara farashin ne a safiyar Talata.
Sun dauki matakin ne a daidai lokacin da gidajen man. NNPCL suka ƙara nasu farashin zuwa N904 a jihar.
A halin da ake ciki dai masu ababen hawa sun yi dogayen layi a gidajen man NNPCL da ke Kano domin shan mai.
Wani jami’i a wani gidan man NNPCL da ke Kano ya shida wa Aminiya cewa suna jiran a ba su umarnin sayar da man a akan sabon farashi.