Isra’ila ta kashe shugaban kungiyar Hezbollah, Nasrallah
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kashe shugahan ƙungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ”Daga yanzu Hassan Nasrallah ba zai sake yi wa duniya ta’addanci ba”.
Kisan nasa na zuwa ne bayan jerin hare-hare cikin dare da Isra’ila ta riƙa kai wa birnin Beirut, da ta ce tana kai wa Nasrallah da sauran kwamandojin ƙungiyar Hezbolla.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, bayan Hassan Nasarallah, an kuma kashe wasu manyan kwamandojin ƙungiyar da ke samun goyon bayan Iran, ciki har da babban kwamandanta mai lura da kudancin Beirut.
Sojojin na Isra’ila sun ce wani jirgin yaƙinsu ne ya kai hari tsakiyar shalkwatar Hezbollah, wanda suka ce yana ƙarƙashin ƙasa a ƙasan wani gida da ke unguwar Dahieh a birnin Beirut.
Sanarwar ta ƙara da cewa an kai harin ne, yayin da ”manyan kwamandojin” ƙungiyar ke gudanar da harkokinsu a wajen unguwar Dahieh da ke kudancin birnin Beirut, wanda yanki ne da ƙungiyar Hezbollah ke da ƙarfi.
Kawo yanzu dai ƙungiyar ba ta ce komai ba game da labarin kisan shugaban nata.