Isra’ila ba za ta iya hana mu kai mata hari ba – Hezbollah
Shugaban kungiyar Hezbollah da ke Lebanon Hassan Nasrallah ya ce babu wani abu da Isra’ila za ta yi da zai sa su daina kai mata hari yankin arewaci inda Yahudawa ‘yan kama wuri zauna suke.
Jagoran yana mayar da martani ne a wani jawabi da ya yi a ranar Alhamis da daddare bayan hare-haren da kungiyarsa ke zargin Isra’ila ta kai ta na’urorin sadarwa da Hezbollah ke amfani da su a Lebanon.
Yayin da yake jawabin Isra’ila ta ce jiragen samanta na yaki sun kai hari kan makaman harba roka sama da dari daya na kungiyar Hezbollah da sauran wuraren da ta kira da ‘yan ta’adda da suka hada da wani rumbun makamai a kudancin Lebanon.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce, ana dab da shirin kai hare-haren rokar ne kan Isra’ila lokacin da jiragen nata suka kai harin. Ba a dai sani ba ko akwai wasu mutane da hare-haren suka ritsa da su.
Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Lebanon ya bayyana cewa Isra’ila ta kai hare-hare akalla 52 a kudancin kasar ranar Alhamis da daddare, kuma ita ma Lebanon ta mayar da martani da inda ta kai hare-hare kan cibiyoyin soji a arewacin Isra’ila.
Tun da farko shugaban na Hezbollah Hassan Nasrallah, ya ce da hare-haren da Isra’ila ta kai ta na’urorin sadarwa da wayoyin oba-oba da suka rika fashewa, ta keta dukkanin wanta iyaka, a tsakaninsu, yana ma zargin Isra’ilar da kaddamar da yaki.