Ina shayar da mijina mama na, yana ƙara mana lafiya da kaunar juna – wata mata
Wata mata mai ‘ya’ya 3 ta bayyana cewa ta na shayar da mijinta man ta, inda ta ce ba iya dankon soyayya ya ke kara musu ba, hakan na karawa mijin nata lafiya.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Rachel Bailey mai shekaru 30, ta na auren Alexander shi ma mai shekaru 30, inda ta baiyana cewa tun a 2017 da Alexander ya fara shan maman ta ba su taba samun sabani ba.
Haka kuma, rahotanni sun ce lafiyar jikinsa na karuwa, kamar yadda jaridar daily Nigerian Hausa na ruwaito.
Da farko dai mijin ya fara shan maman Rachel ne don taimaka mata a yayin da ta ke shayar da yaran su.
‘A yayin da yaron mu, Aria wanda yanzu ya ke da shekaru 6 na ke shayar da shi, Alexender ya fara sha”, inji ta.
Matar ta ce saboda tsiron kamuwa da cutar kansa ne ya sa ta nemi mijin nata ya fara sha mata mama.
Matar ta ce a yanzu mijin nata na shan maman ta sau 3 a rana, inda hakan ya kara musu lafiya su biyun