Labarai

Hawan dutsen Arfa da hawan dutsen dala Kano kwatankwacin ladar su ɗaya a ranar takutaha – Mal. Tahar (Baba Impossible)

Tsohon Kwamishina Dr. tahar baba impossible yana mai cewa duk wanda bai samu damar hawan dutsen arfa da ke kasar Saudi arabiyya ba to idan ya samu hawa dutsen dala dake kano zai samu lada kwatankwacin wanda yaje dutsen arfa.

Dr. Tahar Baba Impossible ya bayyana hakan ne a zantawarsa da gidan rediyo freedom da ke kano inda yake mai cewa.

“Wanda bai samu damar hawa dutsin arfa ba, a ranar takutuha ya hawa dutsen dala kano kamar yaje arfa ne, wannan shiyasa mutane suke tafiya a ranar takutaha sai suje su hau dutsen dala.

Idan kaje kayi kiranta in yana aljannah zaiji shiru, amma idan yana wuta zai amsa, to shi yasa zaka sanya bakinka a rijiyar idan kaji ya amsa to yana wuta, idan bai amsa ba yana wuta- inji baba impossible”

Mutane zasu mamakin taya mutum mai hankali irinsa zai fadi haka to hausawa kance waka a bakin mai ita yafi daɗi.

Ku saurari bayyaninsa a cikin wannan faifain bidiyo.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button