Gwamnatin tarayya za ta saka dala Miliyan $800M a fannin wutar lantarki
Gwamnatin tarayya ta ce ta na shirin zuba jarin dala miliyan 800 domin gina cibiyoyin rarraba wutar lantarki a wani bangare na shirin samar da wutar lantarki na shugaban kasa (PPI).
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mista Bolaji Tunji, mai baiwa ministan wutar lantarki shawara na musamman kan harkokin yada labarai da ya fitar ranar Lahadinan a Abuja.
Tunji ya ce, ministan wutar lantarki, Mista Adebayo Adelabu, ya bayyana haka a lokacin da yayi zuwan gani da ido masana’antar wutar lantarki da rarraba wutar lantarki ta kudancin TBEA a birnin Beijing na kasar Sin.
Ya ce, ministan ya je birnin Beijing domin halartar taron koli na hadin gwiwar Sin da Afirka.
Adelabu ya ce za a raba jarin gida biyu: dala miliyan 400, wanda ya shafi yankunan Benin, Fatakwal, da Enugu Distribution Companies (DISCOs), da dala miliyan 400, wanda ya shafi Abuja, Kaduna, Jos da Kano.
Ya ce duk da koma bayan da aka samu, gwamnati na da burin kara samar da wutar lantarki zuwa megawatt 6,000 a karshen shekara.
Adelabu ya jaddada kudirin gwamnati na hada kai da kungiyoyi masu daraja ta duniya irin su TBEA domin cimma burin Shugaba Bola Tinubu kan harkar wutar lantarki.
Dclhausa