Duk duniya a Nijeriya ne kaɗai a ke yabon ɓarawon dukiyar al’umma – Sanata Ndume
Ali Ndume, sanata mai wakiltar Borno ta kudu, ya ce cin hanci ya zama annoba a Nijeriya saboda ‘yan siyasa da ke satar dukiyar al’umma ana taya su murna kan aikata hakan.
TheCable ta rawaito cewa Sanatan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin ganawa da manema labarai Kano.
Ya kara da cewa, a kasashen da aka ci gaba, mutane na tambayar a ina mutum ya samu kudi, amma a Nijeriya sai kaga ana girmama ka bayan samun dukiyar Haram.
“Babban kalubalen mu a wannan kasar shi ne cin hanci. Har zuwa yanzu, bamu da dokar da zata magance cin hanci a kasar nan”, inji shi.
” Idan kaga wani a wannan tsarin namu, mussaman a siyasa ko gwamnati, kuma ba dan cin hanci bane, to yayi sa’a cewa shi mai tsoron Allah ne.
“A Nijeriya ne kadai zaka saci dukiyar al’umma kuma ka dinga yawon ka ba wata matsala kuma ana yaba maka”, inji shi.