Dalilin da yasa Labarin Hussaina matar Abbas baiyi trending a wajen matan social media
Wani mai amfani da kafar sadarwa ta Facebook kuma marubuci Mohammed Usman ya kawo dalilin da yasa labarin Hussaina matar labari mai sosa zuciya amma baiyi wani tasiri a wajen su ba.
Kamar yadda ya kawo hujjojinsa guda biyar wanda kuma tabbas abun dubawa ne,
Ga abin da yake cewa.
“Ko kun kula da cewa wannan baiwar Allah batayi trending a wajen matan social media sosai ba duk da cewa labarinta labari ne mai sosa zuciya?
Dalilin da yasa labarin baiyi trending ba a wajensu shine kawai :
1. Ita Hussaina mutumiyar kirki ce. Su kuma galibi ba haka suke ba. Mutanen banza ne. Kuma sunfi karkata ga abinda yake na banza kokuma yake dauke da sharri especially akan zamantakewar aure.
2. Ita Hussaina mace ta gari ce wacce tasan mutunci da darajar miji sannan tasan darajar aure. Su kuma galibi ba haka suke ba. Basa ganin aure a bakin komai indai akan son zuciyarsu ne.
3. Ita Hussaina ta yadda akan mijinta ta fuskanci ko wani irin wulakanci. Su kuma galibi basu yadda da hakan ba, saboda basa ganin miji a bakin komai.
4. Ita Hussaina ta yadda ta sadaukar da kome indai akan mijinta ne. Su kuma basu yadda da haka ba. Abinda suka yadda dashi shine, sai dai miji a ko yaushe ya kasance mai sadaukarwa garesu badai su ba.
5. Labarin Hussaina ba labari bane dake nuna rashin mutunci da rashin kirkin maza ga matansu. Su kuma Idan labari baya bayyana maza a matsayin azzalumai marasa kirki, basa so kuma basa kai hankalinsu wajen.
Wayannan sune dalilai da suka sa labarin Hussaina baya trending a wajen galibin mata a social media, especially wayancan yan iskan masu Kiran kansu da Feminists.
Da ace Hussaina labari ta bayar akan, misali, cewa mijinta azzalumi ne. Yana dukanta. Baya ciyar da ita balle tufatarwa. Kokuma ya kashe mata yaya daidai abu makamancin haka, Tabb! Zakayi mamakin yadda abin zaiyi mugun trending a hannun matan social media, especially yan feminism. Zasu kakkara abinda zasu kara sannan suyi ta yadawa a kafa-kafa. Badan komai ba, saboda su bayyanawa duniya cewa ai duk maza haka suke mutanen banza marasa kirki azzalumai.
Zaku yadda dani akan wannan Idan kuka tuna yadda matan social media sukayi ta yuyuyu da yayata labarin karya da aka bayar kwanannan wai wani miji ya saki matarsa tana tsakiyar naquda a asibibitin Aminu kano.
Munafukai!”