Ana makarkashiyar kama Hussaina Iliyasu, matar sojan ruwan da ta yi mana korafin an zalunci mijinta – Ordinary President Ahmed Isah
Ordinary president Ahmed Isah Wanda yake shugaban talabijin din Brekete family tv Radio na kare hakin bil’adama yayi tsokaci akan irin yadda sunka fahimci ana makarkashiyar kama Hussaina iliyasu matar abbas soja.
A cikin tattaunawa da ordinary president yayi da gidan jaridar Dclhausa ya bayyana abubuwa sosai a cikin wannan tataunawa.
Labarin Hussaina iliyasu matar abbas sojan ruwa labarin akwai ban tausai da takaici sosai a cikin wannan labarin irin yadda anka tsare mijin ta tsawon shekaru 6.
Hussaina ta bayar da labarin ta haifi yan biyu har sunka mutu ubansu bai gansu ba, tabbas akwai firgici sosai a wannan labari.
To shine labarin ya karade shafukan sada zumunta wanda shine ake tunanin yau za’a cigaba da bayar da labarin a gidan rediyon Brekete family Radio TV shine yake fadin cewa sun fahimci ana makircin kama ita wanann baiwar Allah, kamar yadda zaku saurara a cikin wannan firar da ankayi da shi.
Ga firar nan ku Saurara.