An yi wa ƴar shekara 17 fyaɗe ta mutu a gonar mahaifin ta bayan biyan N1m kudin fansa
An yi wa wata ɗalibar makarantar sakandare mai suna Habeebah Akinsanya mai shekaru 17 da haihuwa, fyaɗe a a gonar mahaifinta da ke garin Abeokuta, jihar Ogun.
Bayanai sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne a karshen mako a Mile 6, kauyen da ke da tazarar mitoci kaɗan daga gidan talabijin na jihar Ogun, Abeokuta.
Daily Trust ta rawaito cewa mahaifin yarinyar, Akinsanya Aremu, wanda babban jami’in tsaron gwamnati ne, ya kai rahoto a ofishin ƴansanda na Kemta cewa an yi garkuwa da ƴar ta sa yayin da ta ke tsarewa yayar ta shagon POS.
Rahotanni sun bayyana cewa mahaifin ya biya kuɗin fansa Naira miliyan 1 ga waɗanda ake zargi da yin garkuwa da ita, amma duk da haka, su ka kashe yarinyar bayan an mata fade.
An tsinci gawar ta a ranar Lahadi.
Jami’in yansanda na shiyyar Kemta a Abeokuta, CSP Olawale Famobuwa, ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Litinin.
Famobuwa ya ci gaba da cewa, wata mazauniyar unguwar ta ga wani ma’aikacin gona wanda ke aiki da mahaifin marigayiyar sun shiga gonar tare da ita amma sai ta ga ya fito tare da ita ba.
A cewar ta, lokacin da aka tuntubi ma’aikacin, sai ya ce ya bar marigayiyar a gona kuma za ta biyk shi daga baya.
Ya ce daga bisani, ma’aikacin gonar, wanda shi ne babban wanda ake zargi ya gudu.
Daily Nigerian Hausa