Labarai

Akwai yuwuwar farashin man fetur ya haura naira dubu daya ₦1000 – NNPCL

Kamfanin tace albarkatun mai na Najeriya NNPCL, ya ce akwai yuwuwar farashin litar man fetur ya haura naira dubu daya, a wasu daga cikin gidajen mansa da ke fadin ƙasar.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar Litinin din nan, inda ya ce yayi kiyasin hakan ne bisa la’akari da yadda ya suyo mai daga matatar man Dangote a cikin wannan wata na satamba kamar yadda jaridar rfihausa na ruwaito.

Kamfanin NNPCL na tabbatar muku cewa mun sayo mai daga matatar Dangote a watan Satumba ne da Dala, ba naira ba.

Akwai yuwuwar farashin man fetur ya haura naira dubu daya - NNPCL
Jadawalin fashin man fetur Hoto/facebook:NNPC

A cewar sanarwar, farashin litar mai a gidajen mai na NNPCL a jihar Lagos zai kai naira 950, a Sokoto da Abuja 992, a Oyo 960, a jihohin Kano da Kaduna 999, a Rivers 980 sannan a jihar Borno kuma ya kai naira dubu 1,019.

Kamfanin ya ce bisa tanadin dokar da ta samar da kamfanin, ba gwamnati ce za ta kayyaɗe farashin ƙuɗin mai ba, ɓangarorin da abin ya shafa ne ke da haƙƙin hakan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button