Abin tausai : Labarin Ramlat matar soja da ɓata tsawon wata Biyar
Wata Baiwar Allah mai suna Ramlat Ridwan daga jihar kaduna itama ta garyaza gidan rediyon Brekete family tv Radio inda ta samu bada labarinta na ɓacewar mijinta soja na tsawon wata biyar wanda ordinary president Ahmed Isah ne ta samu mika sakonta.
Ramlat Ridwan matar Hamza B.I tazo je ne domin bada labarin bacewar mijinta da yake aikin sojan ruwa “Navy” Kenan inda ta bada labarin bacewar mijinta da ya share shekaru yana aikin soja.
A cikin wannan labari babban abin da zai baka mamaki shine irin yadda Hamza B.I ya shafe shekaru fiye da goma a cikin wannan aiki amma kuma , kwatsam ɓacewarsa tazo da barazana ga iyalinsa wanda sunka yi nema a gayamusu gaskiyar lamarin.
Daga karshe anka basu sakamako wanda tabbas wannan akwai alamun rashin gaskiya da ha’inci a cikin martanin da anka baiwa iyalinsa a daidai lokacin da mahaifinsa take da ciwon hawan jini.
Ga bidiyon nan ku saurara