Labarai

ABIN A YABA: Masu shirin ‘Fashin Baki’ sun baiwa sojojin da suka kashe Halilu Sububu, Naira miliyan 1.8

Masu gabatar da shirin nan na Fashin Baki, wani shiri da ake yi ta shafin Facebook na mako-mako, sun sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 1.8 ga sojojin da suka kashe fitaccen dan fashin dajin nan, Halilu Sububu a jihar Zamfara.

Daya daga cikin masu gabatar da shirin, Bulama Bukarti, ne ya sanar da tallafin a madadin takwarorinsa, Jaafar Jaafar, Nasiru Zango da Abba Hikima, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a jiya Lahadi.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa an kashe Sububu tare da mayakan sa a wani samame na hadin gwiwa da sojojin kasar suka kai a garin Kwaren Kirya da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a ranar Alhamis.

A watan Mayu ne dai rundunar sojin Najeriya ta sanya ladan Naira miliyan 5 ga wanda ya gano inda Sububu ya ke wanda ta ke nema ruwa a jallo.

Haka zalika da ya ke yabawa sojojin bisa nasarar da suka samu, babban hafsan hafsoshin tsaro, Chris Musa, ya basu kyautar Naira miliyan daya su raba a junan su, inda kowa zai samu Naira dubu 38.

Sai dai kuma a ganin Jaafar da Bukarti ladan ya yi kadan matuƙa, musamman duba da irin girman ba ya sadaukarwar da su ka yi.

Hakan ne ya sanya masu gabatar da shirin su hudu su ka hada Naira miliyan 1.8 su ka baiwa sojojin sannan kuma su ka yi kira ga ƴan Nijeriya da su bada nasu gudunmawar domin taimakawa sojojin da iyalan su sakamakon gagarumar gudummawa da suka bayar wajen yaki da ta’addanci.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button