ZANGA-ZANGA: Masu gadi 800 mu ka ɗauka aiki don tsare kasuwar mu — Dawanau
Ƙungiyar ƴan kasuwar hatsi da kayan abinci ta Dawanau a Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano ta ɗauki matakan kare kasuwar ta hanyar ɗaukar masu gadi 800 aiki.
Shugaban ƙungiyar yan kasuwar, Alhaji Muntaka Isa ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a yau Litinin.
Ya bayyana irin kokarin da gamayayyar jami’an ƴan sanda da sojoji suka yi wajen tabbatar da tsaro a jihar.
Ya kara da cewa sun kara ɗaukar masu gadi 400 wadanda ke aiki tare da jami’an tsaro wajen bada kariya ga kasuwar.
Acewarsa, kasuwar ta fuskanci barazana daga ɓata gari daga unguwannin Kurna da Bachirawa wadanda suka yi yunkurin afkawa a yayin zanga-zanga.
Shugaban kasuwar ya bukaci mazauna unguwar da su taimakawa jami’an tsaro da bayanai kan duk wani yunkuri na ɓata garin.
Daily Nigerian Hausa