Labarai

‘Yan siyasar Nijeriya na siyasantar da matsalar tsaro a ƙasar –Ngozi Okonjo-Iweala

Babbar daraktar Ƙungiyar kasuwanci ta duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta zargi wasu ‘yan siyasar Nijeriya da siyasantar da matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Yayin da take jawabi a taron shekara-shekara da ƙungiyar lauyoyin ƙasar ta shirya a birnin Legas a ranar Lahadi, tsohuwar ministar kuɗin ta ce tsaro ne ginshiƙin samun kowane irin ci gaba a ko’ina.

Ta ce ba za’a samu ci gaban tattalin arziki idan babu tsaro ba, haka kuma ba za’a samu tsaro ba dan ba mu da ci gaba ba.

Ta kuma yi zargin cewa akwai ‘yan siyasa a Nijeriya da ke tunanin cewa hanyar da kawai za su bi wajen hana abokan hamayyarsu jin daɗin mulki, shi ne ƙirƙirar musu matsalar tsaro, ba tare da la’akari da asarar rayuka da dukiyoyin al’umma da ba su ji ba su gani ba.

Tace abin da muka sani shi ne ‘yan siyasar ƙasarmu sun siyasantar da matsalar tsaro a ƙasarmu don cimma burinkansu na ƙashin kai, wannan kuma shi ne ya jefa ƙasarmu halin da take ciki a yanzu.

Sanna kuma ta yi kira ga ‘yan siyasar ƙasar su daina siyasantar da matsalar tsaro ta hanyar alaƙanta ta da abokan hamayyarsu na siyasa.

Dclhausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button