Labarai

Uefa ta karrama Ronaldo a matsayin wanda ya fi cin ƙwallo a tarihin Champions League

Cristiano Ronaldo ya samu lambar yabo ta kasancewa gwarzon ɗan wasan da ya fi zura ƙwallo a tarihin gasar Zakarun Turai ta Champions League.

Shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Turai, Uefa, Aleksander Ceferin wanda ya miƙa wa Ronaldo kyautar a lokacin bikin fitar da jadawalin ”gasar da ta fi muhimmanci,” in ji shi – Champions League, yau a birnin Monaco, na Faransa.

Ceferin ya ce an karrama Ronaldo da kyautar ne saboda babban tarihin da ya kafa a gasar ta Zakarun Turai.

Uefa ta karrama Ronaldo a matsayin wanda ya fi cin ƙwallo a tarihin Champions League
Cristiano Ronaldo

Cristiano Ronaldo ya ce sabuwar kyautar da aka ba shi za ta samu muhimmin waje a dakinsa na adana kayan tarihi a Madeira.

Ɗan wasan na gasar Saudiyya

Shugaban na Uefa, ya kuma ce Gianluigi Buffon, wanda yana daga cikin masu fitar da jadawalin na yau, ya ce shi ne gwarzon mai tsaron raga a duk duniya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button