Labarai

Tsada Rayuwa: Ina gurin da zan saye fulawa kafin azo kaina ta sami karin Dubu ashirin ₦20,000

A cewar wani mai siye da siyarwa mai suna Malam Haruna Chairman wanda yaje domin ya yi sari a kasuwar ta singa.

Ya shaidawa Rahma cewa lokacin da yaje kasuwar ana sayar da buhun fulawa Dubu 63,500 sai dai yace yana tsaye a layi kafin azo kansa ta koma Dubu 82,000 kuma tsohon kaya ne,

Ya shaidawa Rahma Radio da Talabijin yadda `yan kasuwar suka kara dubu Ashirin 20 a lokaci guda.

Wani labari: Hankalina yayi matuƙar tashi da naga karin kuɗi kayan abinci a soshiyal midiya – Abba kabir Yusuf

Gwamnan yayi wannan tsokaci ne yayin ganawar gaggawa ta musamman da yan kasuwannin Jihar Kano akan tashin gwaron zabi na kayan masarufi a kano.

Yace karin kudin Abinci daga kasuwar Singa zai shafi hatta wasu jihohin a Arewacin Najeriya.

Gwamnan ya kuma nusar da yan kasuwar da su sani cewa irin wannan matsin rayuwa da tsadar kayan abinci,sune suka tunzura matasa suka fita zanga zanga.

A karshe dai yan kasuwar sunyi alkawarin cewa za’a ga sauyi daga wannan rana.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button