Labarai

Shugaba Tinubu ya amince da dawo da biyan tallafin man fetur

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da buƙatar da kamfanin mai na ƙasa, NNPC ya aike masa na dawo da biyan tallafin man fetur.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa NNPCL ya nemi Tinubu da ya sahale ya biya ribar da ya samu ta 2023 a matsayin tallafin mai a maimakon ya saka kudin a asusun gwamnatin taraiya.

A rahoton da TheCable ta wallafa a yau Litinin, Tinubu ya bada umarnin ne bayan da NNPCL ya nuna cewa ya ƙarar da duk wasu hanyoyi da zai bi ya riƙa samar da daidaito a farashin mai a ƙasar.

“Saboda haka Tinubu ya ba NNPC umarnin amfani da harajoji da riba da sauran kuɗaɗe da ya samu wajen biyan tallafin mai maimakon asusun gwamnati,” in ji rahoton.

Daily Nigerian Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button