Sautin Murya: wata Jaruma gudu da naira dubu Dari biyu ₦200,000 – furodusa
Shahararriyar yar fim ɗin Hausa Zahra’u Saleh Pantami (Adaman Kamaye), ta tsere da kudi naira dubu 200 na Furodusa lsah Umar (Turakin Kongo) bayan da aka bata kudin ta bai wa Diamond Zahra da nufin zuwa aikin wani fim mai suna Takaddama.
Furodusan ya bayyana cewa ya ɓukaci lambar jaruma Diamond Zahra ne domin ta zo jihar Nasarawa wajen aikin fim, nan take Adaman ta ce ta san ta kuma za ta kira ta don zuwa aikin.
Bayan sakar mata ragamar tattaunawa da jaruma Diamond, Adaman Kamaye ta ce sun shirya naira dubu 200, inda nan take ta umurci furodusan da ya ba ta kudin don ta tura mata.
Bayan ya sunna mata kudin tun daga lokacin ta ce yau ne gobe ne za ta zo duka dai ana yi mata uzuri saboda ana tare, a cewar furodusan.
Bayan Adaman ta kammala aikinta aka sallame ta tare da alkawarin cewa Diamond Zahra za ta zo gobe ko jibi shiru babu labari, daga bisani aka tuntubi Diamond Zahra inda ta bayyana cewa Adama ta kira ta akan za ta yi aiki amma ta ce mata ba za ta iya zuwa ba saboda dalilai na tsaro.
Daga ƙarshe Adaman Kamaye ba ta daukar wayar furodusan don jin inda kudin sa ya makale.
Saurari cikakken bayyani a nan.