Riga-kafin yara da kula da mata masu juna-biyu hakki ne a kan kowa – Ali Nuhu
Shugaban hukumar kula da harkokin fina finai ta Nijeriya kuma fitacce jarumi a masana’antar shirya fina finai ta KANNYWOOD, Ali Nuhu Muhammad ya ce iyaye da al’umma nada rawar da zasu taka wajen magance yawan mace macen mata a yayin haihuwa da mutuwar kananan yara.
Haka kuma ya bayyana cewa jaruman shirya fina finai ma na da rawar da zasu taka wajen wayar da kan al’umma kan abubuwan da suka shafi, rigakafi da yaki da cutar shan inna da kalubalen yaran da bas zuwa makaranta.
Ali Nuhu na bayanin hakan ne yayin ganawa da manema labarai bayan kammala taron da asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya, UNICEF, ya shirya da masu ruwa da tsaki kan magance kalubalen rigakafi da yaran da basa zuwa makaranta da matsalolin mata da sauransu a Kano ranar Talata.
Ya ce a matsayinsa na jakadan UNICEF suna iya ka kokarinsu wajen wayar da kan al’umma.
“Kasancewa ta jakadan UNICEF na duniya, ina abubuwa da dama tare dasu. Kuma zan ci gaba da taka rawa. Ina fadakarwa a shafukan sada zumunta, dukkan bayanan da suke wajena ina kokarin isar da su.
Ali Nuhu ya kuma kara yin kira ga iyaye wajen kula da rigakafin ‘ya’yansu inda ya bayyana cewa rigakafi yafi magani.
” Abu ne da ya dace ga mutum ya dinga kai ‘ya’yansa rigakafi kafin komai. Wasu yaran suna ganin baiken iyayensu idan suka girma saboda sun gaza wajen kula dasu suna kanana.
Sannan yayi kira ga gwamnatoci da su mayar da hankali wajen inganta cibiyoyin lafiya a matakin farko don kula da mata da kananan yara.
Daily Nigerian Hausa