Labarai
Bidiyo: Na kwanta da maza sama dubu uku, in ji jarumar Nollywood ,Esther
Jaruma a masana’antar shirya finafinai ta kudancin Nijeriya, Nollywood, Esther Nwachukwu ta bayyana kalamai masu cike da tababa kan rayuwarta ta mu’amala da maza.
A wata tattaunawa a wani shirin rediyo mai taken Honest Bunch, ta bayyana cewa bata san adadin mazan da ta sadu dasu ba, inda ta kiyasta cewa za su kai dubu 3.
Sannan ta kuma ce tana saduwa ne kadai da mazajen da suke da aure daga kasashe kamar Najeriya da Cyprus da Turkey da Kenya da Ghana.
Da me yi mata tambayoyi a shirin ya tambaye ta “maza nawa kika taba kwanciya da su?” sai Nwachukwu ta bada amsa: “ban san adadin au ba”.
Sai mai gabatarwar ya tambaye ta; “Shin sun kai dubu?”, sai ko ta kada baki ta ce, baza ta iya lissafawa ba inda ta ce sun haura dubu 3.
Ga bidiyon nan ku kalla.