Labarai

Matsalar Tsaro : Ana jimamin kisan Sarkin Gobir yan bindiga sun sace sama da mutane 150 a Masarautar Gobir

Bayan kisan gillar da aka yiwa Sarkin Gobir Alhaji Isa Muhammad Bawa, ‘yan bindiga sun sake sace wasu mutane sama da 150 a yankin Gobir a daidai lokacin da ake jimamin mutuwar Basaraken.

Farfesa Bello Bada na Jami’ar Usman Dan Fodio dake Sokoto ya bayyana wannan a tattaunawar da ya yi da RFI Hausa ta fezbuk, ya yin da yake danganta matsalar ‘yan bindigar da sakaci daga bangarori da dama.

Shehun malamin ya ce wannan sakacin ne ya sa har wasu ‘yan bindiga suka yi ikrari da kuma barazanar kama shugaban kasa Muhammadu Buhari lokacin da yake karagar mulki.

Farfesa Bada ya ce wannan ba shi ne karo na farko da ake kai hari ga manyan sarakuna ba, sai dai wannan shi ne karo na farko da aka yiwa babban Basarake kisan gilla.

Shehun malamin wanda ya danganta kisan a matsayin wulakanci ga daukacin Najeriya, ya ce lokaci da ya yi jama’a za su sake tunani a kan illar wannan matsalar ta ‘yan bindiga dake kashe mutane ba tare kaukautawa ba.

Bada ya ce an taba kai irin wannan harin a kan tawagar Sarkin Potiskum a hanyar Zaria inda ya sha da kyar, ya yin da shi ma Sarkin Kauran Namoda ya tsallake rijiya da baya, ya yin da aka hallaka ‘yan tawagarsa.

Farfesa ya ce a kasar Zuru ma an taba yiwa wani Basarake yankar rago, amma da zaran an kwan biyu sai mutane su manta kamar ba’a taba yi ba, sai kuma an sake wani harin.

Shehun malamin ya ce bai da ce ace an kauda kai wannan matsala na ci gaba da faruwa ba alhali an san masu aikata laifin, an kuma san inda suka fito amma kuma an ki daukar matakan da suka dace.

A na shi gudumawar da ya bayar a shirin, masanin harkar tsaro Dakta Yahuza Getso ya bukaci hukunta manyan jami’an tsaron da ake zargi da sakacin da ya kai ga kashe Sarkin Gobir bayan kwashe sama da makwanni 3 a hannun ‘yan bindiga ba tare da wani yunkuri na kubutar da shi a zahirance da jama’a suka gani, baya ga batun biyan diyya.

Getso ya ce akwai barazanar samun barkewar rikicin kabilanci tsakanin mazauna wannan yanki na Sokoto sakamakon wannan kisan gillar, ganin yadda matsalar ‘yan bindigar ke rarraba kawunan kabilun dake yankin na Gobirawa da Fulani da kuma Hausawa.

Masanin harkar tsaron ya ce an san shugabannin ‘yan bindigar da suke wannan yanki na arewa maso yamma, an san garuruwan da suka fito, an kuma san iyayen su da kuma masu kai musu kayayaykin da suke bukata.

Farfesa Bada da Dakta Getso duk sun amince da cewar jami’an tsaron suna da kwarewar da za su iya tinkarar wannan matsala kuma su ga bayan ta, amma ga alama shugabannin siyasa ba sa ba su gudumawar da suke bukata domin shawo kan matsalar.

-Rfihausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button