Matsalar Tsaro: Al’umma gari sun hallaka ƴan bindiga 37 a Zamfara
A wani mataki na kare kai, mazauna kauyen Matusgi da ke karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga 37 da suka mamaye al’ummarsu da shirin sace mutanen yankin.
Rahotanni daga wani mazaunin garin na cewa, ‘yan bindigar sun isa kan babura da misalin karfe biyu na rana. a ranar Laraba, sun fuskanci turjiya mai tsanani ga al’ummar yankin.
Mazauna kauyen, dai sun shirya kansu ne ta hanyar amfani da makaman da aka kera a cikin gida da kuma na gargajiya domin kare kansu, Daily Nigerian Hausa na ruwaito.
Wannan dai ba shi ne karon farko da su ke kare al’ummarsu ba, amma wannan shi ne karo na farko da suka yi irin wannan gagarumin farmaki ga maharan.
Da farko dai ‘yan bindigar sun yi yunkurin tursasa mutanen kauyen ta hanyar harbi da bindiga da isar su kauyen. Duk da haka, mutanen ƙauyen, sun shirya don mayar da martani ta hanyar kare kai.
Bayan wani kazamin fada da aka dauki tsawon awanni ana yi tsakanin al’ummar da ‘yan bindigar an tilastawa ‘yan bindigar ja da baya, inda suka bar ’yan uwansu guda 10 da suka mutu.Duk da haka mutanen kauyen ba su karaya ba, suka sake haduwa suka yi wa ‘yan bindigar kwanton bauna.
Saurari rahoton Dclhausa a cikin sautin murya.
A lokacin da ‘yan fashin suka yi yunkurin sake haduwa suka dawo, sai mutanen kauyen suka sake kai hari, wanda ya kawo adadin ‘yan bindigar da aka kashe zuwa 37.
Hakimin Matusgi, Alhaji Ciroma Muhammad ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya kuma ce mutanen kauyen uku ne suka rasa rayukansu a arangamar. Ya kara da cewa al’ummomin da ke makwabtaka da su sun ba da rahoton ganin ‘yan bindigar na jigilar gawarwakin ‘yan uwansu da suka mutu a kan babura.
Wannan shi ne hari na 13 da wadannan ‘yan bindiga suka kai kauyen na Matusgi in ji Alhaji Muhammad. “Makonni uku kacal da suka wuce, sun yi garkuwa da mazauna kauyen 23, yawancinsu mata, ba tare da yin harbi ba har sai da suka fita. An kiyasta kudin fansa kan Naira 150,000 ga kowane mutum, amma kawo yanzu an saki mata bakwai, sauran kuma har yanzu suna tsare a wajen su.