Labarai
Masu zanga-zanga sun shiga har gidan Buhari a Daura


Advertisment
Masu zanga-zanga sun kutsa gidan tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yau a lokacinda ake zanga-zangar yunwa da tsadar rayuwa
Rahotanni sun ce daƙyar aka rarrashi fusattatun matasan yayin da suka nemi farfasa gidan, inda aka rarrashe su aka sanya suka gabatar da mutum ɗaya a cikinsu ya yi jawabi ana daukarsa a kyamara tare da yarjejeniyar za a turawa shugaba Tinubu,
Jaridar A Yau ta ruwaito daga nan sai matasan suka nufi fadar Sarkin Daura da Magajin Garin daura inda suka yi ɓarna daƙyar gamayyar jami’an tsaro suka tarwatsa masu zanga-zangar waɗanda ke ta ihu “Bama yi, Bama yi, Bama yi”
Yanzu haka dai an ƙara tsaurara tsaro a gidan tsohon Shugaban kasar da masarautar Sarkin Daura da sauransu
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




