Kannywood
Maryam Labarina: Dalilin da yasa na furta kalamai da basu dace akan bidiyo dina dake “trending”- Fatima Hussaini
A lokacin da nake live akwai wajen da mutane suke mayar da martani a turance ana kiransa “comments” to nan ne wani yacemin
” Dallah can mu bamu gane abin da kike fadi ba, turancin dole ne kiyi mana hausa”
To ga duk wanda ya kalli live bidiyon nayiwa wancan martani ne da yayi wannan magana, to naga ana cewa nace kaza nace kaza ni ba haka nake nufi ba.
Jaruma fatima Hussaini wadda anka fi sani da maryma labarina matar Alhaji al’amin mainasara ta nuna a lokacin da take wannan live mutane basu wuce su dari biyar ba.
Fatima Hussaini ta janye kalamanta kuma tayi kira ga mutanen da basu fahimci abun ba tana mai bada hakuri.
Zaku ji cikkaken bayyani daga bakin ta.