Labarai

Kukan Ɗadi: Mace Me cin dusa ta samu tallafi , Ga al’umma (bidiyo da hotuna)

Alhamdulillah, bayin Allah sun yi matukar kokari, an tarawa baiwar Allah nan kudi Naira dubu Dari Tara (900k) ga kuma kayan abinci buhun shinkafa biyu da buhun gari ga taliya da Macaroni da katan din omo da sabulu da sauran kayan abinci.

Mun yanke shawara kudin za mu samu karamin gida ko mai daki daya ne a sai mata domin ta huta da haya, idan Allah ya aa kuma an samu karin kudin sai a sai mai daki biyu.

Bani da bakin da zan godewa bayin Allah da ke taimakawa duk lokacin da muka bukata, har da masu taya mu sharing har a samu taimakon, Allah ya faranta muku duniya da lahira amin, Allah ya fidda ku daga dukkan kunci ku da iyalinku, amin ya Allah.

Ga bidiyon da take cin dusa.

KAR KU KULA DA KALAMAN MATARNAN, KU TAIMAKA MATA DON ALLAH DOMIN CIWON DAMUMA, (Depression) NE TA KAMATA.

Tun kwanaki wata baiwar Allah ta je gurin mahaifiyata ta sanar da ita halin da suke ciki na matsi sa yunwa tuwon dusa suke ciki da yaranta, mijinta ya gudu ya barta, sai na ce ta yi vedio ta turo, sun turo vedio din na ga bai yi ba, amma na shaafa ban yi saving lambarsu ba balle na ce su gyara.
Jiya mamana ta kuma kirana ta ce mun matarnan me cin dusa fa sun dawo suna ta rokonta, amma ta ce su je su name ni, sai na ce mata naga vedio din su bai yi bane, a gaya musu su kirani zan gaya mata yadda za ta yi, ta rufe jikinta, kuma duk da tana cikin damuwa, domin kamar depression ne ya kamata amma ta gyara kalamantan sun yi nauyi da yawa, to kawai sai na ci karo da vedio din yanzu yana yawo, wasu na zaginta, wasu na gaya mata magana, wallahi matanmu da yawa suna cikin wannan masifar da ko tsarin iyalin ka ce su yi ba su da ilimin yi, balle su san yadda za su kula da kansu, ga yaya ga yunwa ga talauci, ga mazajan sun gudu sun barsu, idan sun samu dama su kara dawowa su lallabasu su kara musu ciki, mu da muke mu’amala da wadannan matanne kadai mu ke gane halin da su ke ciki, sai dai ka zaunar da su ka musu bayani bayan ka taimaka musu, wasu da yawa rashin galihu da talauci da rashin ilimi ke kai su ga wannan rayuwa, don haka idan baka cikin irin rayuwar ba za ka gane ba.

Don haka don Allah, indai kun yi niyyar taimakonta ku yi hakuri domin suna cikin masifa ita da ya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button