Labarai

Jirgin ruwa ya kife da mutane a jihar Sakkwato da yayi sanadiyar mutuwa mutane da ɓacewar wasu da dama

Ana ci gaba da aikin ceto rayukan wasu ‘yan Najeriya da akalla ba zasu rasa kai goma sha uku ba a wani hadarin jirgin ruwa da ya auku jiya Lahadi a Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya.

Jirgin kwalekwale ne na katako dauke da mutane fiye da 35 ya nutse, inda kawo yanzu ake aikin lalabo gawarwakin wadanda suka mutu cikin ruwan.

Hadarin ya auku ne agarin Dundaye na karamar hukumar Wamakko a jiahr Sakkwato a cikin gulbin Rima wanda ke dauko ruwa daga madatsun ruwa na Bakalori ta jihar Zamfara da Goronyo ta jihar Sakkwato.

Mutanen da suka hada da manya da yara, maza da mata sun shiga kwalekwale a tsallaka ruwan da su, su je aiki cikin fadama.

Muhammad Bello wani dattijo ne wanda gaban sa lamarin ya faru, ya ce jirgin ya dauki mutane fiye da kima kuma sai da mai tukin jirgin ya so mutane su rage suka ki.

Bayan ya tashi ya hau ruwa yana kai tsakiya sai ya soma kwasar ruwa daga nan sai ya nutse, amma dai a cewar sa an samu ceto wasu da rayuwa.

Wakilin Sarkin Adar na Dundaye Muhammad Bello Hassan yana daga cikin muhimman mutane da suka fara zuwa wurin bayan samun labarin nutsewar jirgin, ya ce mafi yawan wadanda abin ya rutsa da su zasu je ne wurin yin kayan wuta da kuma aikin kalar shinkafa., kamar yadda voahausa na ruwaito.

Saurari cikakken rahoton a nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button