Har yanzu dokar hana shigo da shinkafa ta kan iyakokin tsandauri na aiki – Kwastam
Hukumar Kwastam ta Ƙasa ta ce umarnin shugaban ƙasa Bola Tinubu na shigo da kayan abinci ba tare da karɓar haraji ba, bai haɗa da shigo da shinkafa ta kan iyakokin tsandauri ba.
Da ya ke jawabi ga manema labarai, Kwanturola Janar na Kwastam na ƙasa, Bashir Adeniyi ya ce babu wani abu da ya sauya game da shigo da shinkafa, inda ya ce umarnin gwamnatin tarayya ya bada damar shigo da samferar shinkafa ne kawai ta bodojin tsandauri.
“Babu wani da ya sauya game da shigo da shinkafa. Babu wani da ya ce a shigo da shinkafa ta hanyar kan iyaka ta kasa. Babu abinda ya sauya game da shigo da shinkafa.
” Idan aka dauke maganar danyar shinkafa wacce ba a gyara ba, wannan shi ne kawai gyaran da aka yi. Amma manufar hana shigo da shinkafa tana nan.
“Har yanzu akwai haramcin shigo da shinkafa ta kan iyakokin kasa”, inji Adeniyi.
Sakamakon tashin gwauron zabi da kayan abinci yayi, shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin shigo da kayan abinci ba tare da karbar haraji ba.
A umarnin da shugaban kasar ya bayar ya ce za a shigo da kayan abincin ne ba tare da karbar haraji ba na tsawon kwanaki 150.
-Daily Nigerian Hausa