Haɗama ko Talauci : Ma’aikatan gwamnati a Kaduna sun koma crypto
A yayin da gwamnatin jihar Kaduna ke jan kafa wajen aiwatar da mafi karancin albashi na Naira dubu 70, mazauna jihar, ciki har da ma’aikata sun rungumi harkar rypto a matsayin wata hanya na samun kudade.
Wakilin Daily Trust ya lura cewa, an samu karuwar masu yin Crypto a Kaduna ga wadanda ke amfani da wayoyin hannu na zamani.
Hakazalika Daily Trust ta gano cewa ma’aikata daga ma’aikatun ilimi da ayyuka da fannin shari’a sun rungumi ‘mining’ na crypto a matsayin wata hanya ta daban ta samun kudade.
Wani ma’aikaci a ma’aikatar shari’a da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ” na shiga harkar crypto tsawon watanni a matsayin karin hanyar samun kudi, mussaman tun da gwamnatin jiha har yanzu ba ta aiwatar da tsarin mafi karancin albashi ba.
” Na samu nasarar samun Naira dubu 100 daga Crypto a ranar Lahadi da ta gabata”, in ji shi.
Shima wani ma’aikaci daga hukumar KASTLEA, wanda ya samu Naira dubu 80 daga crypto a ranar Lahadi ya ce “ina yin crypto ne domin samun karin kudi daga wanda na ke karba duk wata a matsayin albashi. Wata hanya ce wacce ba ta hana ni aiki na”, inji shi.
Shima wani mai suna Haruna da ke aiki a wani kamfanin Inshora mai zaman kansa ya samu Naira dubu 200 daga kudin na Crypto.
” Zan yi amfani da wani bangare na kudin na siyi kayan abinci”, inji shi.
Daily Nigerian Hausa