Farashin abinci ya fara sauka a wasu kasuwannin arewancin Nijeriya
Yayin da aka faragirbi a wasu sassan Nijeriya, ana sa ran za a iya samun saukar farashin amfanin gona a jihohin Kano, Kaduna da Katsina.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN, ya bayyana cewa farashin kayan masarufi ya ragu a sassan jihar Kano, da kuma Zaria da Kafanchan a jihar Kaduna.
Sai dai NAN ta bayyana cewa wasu daga cikin kayayyaki sun ci gaba da yin tsada a sassan birnin Kaduna da jihar Katsina.
Binciken da ta gudanar a jihohin uku ya nuna cewa abubuwa da dama ne suka haddasa sauye-sauyen farashin kayan abinci.
A jihar Kano, farashin kayan abinci ya ragu a daidai lokacin da sabbin kayan amfanin gona suka fara isa kasuwanni.
Bincike ya nuna cewa farashin hatsi ya ragu.Sai dai shinkafar gida da aka fi amfani da ita, tana ci gaba da yin tsada, inda buhu ya tashi tsakanin N150,000 zuwa N170,000.
Ana sayar da buhun masara akan N95,000 sabanin N105,000,haka kuma buhun gero da ake sayar da shi kan Naira 90,000, yanzu ya koma Naira 80,000.
Buhun wake da a baya ake sayar da shi tsakanin N170,000 zuwa N180,000 ana sayar da shi kan N130,000, ya danganta da ingancinsa kamar yadda binciken ya bayyana.
An sayar da buhun gyada tsakanin N150,000 zuwa N170,000 sabanin N200,000,bugu da kari, farashin tumatur ya yi tsada a Kano yayin da farashin albasa shima ya yi tashin gwauron zabi.
Dclhausa